Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Kafin Ka Fara Blogging a Najeriya
![]() |
| Hoton mata shi yana yana rubutu dakuma aiki da komfuta. |
Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Kafin Ka Fara Sana’ar Blogging A Nijeriya
Blogging aiki ne na hakuri. Ba saurin kudi ba ne. Wanda ya shigo da tunanin yau ya wallafa, gobe ya samu riba, zai gaji da wuri. Idan kana son daukar blogging da muhimmanci, ka dauke shi a matsayin sana’a.
Ga abubuwa 5 da dole ka fahimta tun kafin ka fara.
1. Blogging ba wasa ba ne, aiki ne mai tsari
Yawancin masu farawa suna daukar blogging kamar rubutu kawai. Wannan kuskure ne.
Blogging yana bukatar:
Tsari mai kyau
Lokaci a kai a kai
Ilimi akan SEO
Fahimtar bukatar masu karatu
Google AdSense yana duba blog din ka a matsayin business. Idan babu tsari, babu damar amincewa. Ka dauki blog din ka kamar kamfani, ba kamar shafin wasa ba.
*THE-ILLUSION-OF-OVER-NIGHT-SUCCESS....
2. Abun da kake rubutawa yafi muhimmanci fiye da yawan rubutu
Rubutu da yawa ba yana nufin inganci ba. Google yana son rubutu mai amfani.
Ka tambayi kanka:
Wannan rubutun zai taimaki mai karatu kuwa
Shin yana amsa tambaya daya ko fiye
Shin ba kwaikwayo bane daga wani shafi
Rubutu mai kyau:
Yana da taken da ya fito fili
Yana da sassa masu tsari
Yana da kalmomi masu saukin fahimta
Idan kana son AdSense, ka guji:
Copy and paste
Rubutu marar ma’ana
Taken karya don jan hankali
3. Hakuri shine jigon nasara a blogging
A Nijeriya, yawanci blog yana daukar watanni kafin ya fara samun zirga zirga. Wasu ma suna daukar shekara.
"IMANI-DA-JURIYA-KE-SAMAR-DA-NASSARA...
Gaskiya itace:
Ziyara ba zata zo da wuri ba
AdSense ba zai amince da kai nan take ba
Kudi ba zai shigo da sauri ba
Wanda ya yi nasara:
Yana rubutu ko babu views
Yana gyara kuskure a hankali
Yana koyo kullum.
Idan baka da hakuri, blogging ba naka ba ne.
4. Ka san dokokin Google AdSense tun daga farko
Yawancin blog a Nijeriya suna faduwa AdSense saboda sakaci.
Abubuwan da Google ke bukata:
Privacy Policy
About Us
Contact Page
Rubutu mai tsafta, babu batsa ko damfara
Babu spam links
Ka guji:
Click bait
Abubuwan karya
Hotuna ba tare da izini ba
Google yana kallon amincewa. Idan ya ga ka na gina blog da gaskiya, damar ka na karuwa.
5. Ka rubuta domin mutane, ba domin robot ba
SEO yana da muhimmanci, amma mutane sun fi muhimmanci.
Rubutu mai ja hankali:
Yana magana kai tsaye da mai karatu
Yana amfani da misalai
Yana da saukin karantawa
Mai karatu idan ya ji an fahimce shi:
Zai dade a shafi
Zai dawo
Zai raba rubutun
Wannan shine abin da Google ke so.
Karfafa gwiwa ta gaskiya
Idan ka fara blogging yau:
Kada ka kwatanta kanka da manya
Kada ka gaji da jinkiri
Kada ka yi karya don kudi
Duk babban blogger ya fara daga sifili. Bambanci daya ne, hakuri da juriya.
Idan kana cikin shiri yin aiki, ka dage, ka gyara kusakuran ka, blogging a Nijeriya yana da makoma.
HANYOYI-GUDA-3-DOMIN-DAINA-JIN-KASALA...
Fadi abin da kake bukata kai tsaye.
