BASHAR IMPACT SOLUTION

Inspiring Change, Creating Impact Through Digital Excellence

SELF-CONTROL

self control and inner peace amidst distractions

Concept of self-control and inner peace amidst worldly distractions.

Yadda Zaka Zama Mutum Mai Kamun Kai (Self-Control) A Zamanin Fitina

A cikin duniyar yau da aka kewaye mu da abubuwan shagala, hotuna, da bidiyoyi masu janye hankali, zama mutum mai kamun kai babban kalubale ne. Kamun kai ba wai kawai dabi’a ce ta kwarai ba, babban makami ne da yake kare mutuncinka, imanninka, da kuma makomarka. Idan baka iya mallakar zuciyarka ba, wasu abubuwa zasu mallake ka.

1. Fahimtar Hatsarin Shagala

Zamanin nan na intanet ya kawo fitintinu da dama da suke janye matashi daga manufarsa. Kamun kai yana farawa da sani. Ka fahimci cewa ba kowane hoto ko bidiyo ya dace ka kalla ba, kuma ba kowace tattaunawa ya dace ka shiga ba. Mutum mai kamun kai yana da tacewa a zuciyarsa wacce take gaya masa: "Wannan ba zai amfane ni ba."

2. Karfafa Alaka Da Ubangiji

Babu abin da yake taimaka wa mutum ya mallaki kansa kamar jin tsoron Allah a boye da sarari. Imani yana zama birki wanda yake tsayar da kai a duk lokacin da sha’awarka ko shaitan suka yi kokarin janye ka zuwa ga barna. Yawaita ambaton Allah da kiyaye sallah suna ba zuciya karfi na cewa “A'a” ga abubuwan da basu dace ba.

3. Horar Da Kai A Kan Juriya

Kamun kai yana bukatar horo. Ka fara da kananan matakai. Rage lokacin da kake batawa a kafofin sada zumunta. Ka tsara lokacin karatu. Ka dage akan abin da ya fi amfani. Wadannan matakai suna gina karfi a hankali. Lokacin da babban kalubale ya zo, zaka samu juriyar tsayawa.


READ-THIS: THE-ILLUSSION-OF-OVERNIGHT-SUCCESS:WHY-SUSTAINABLE-GROWTH-REQUIRES-PATIENCE.